Connect with us

Featured

Haɗakar Atiku da Obi Ba Za Ta Kayar da Tinubu a 2027 ba – Festus Keyamo

Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da jita-jitar cewa haɗin gwiwa tsakanin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar da ɗan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi, zai iya kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

Ministan Sufurin Jiragen Sama da Cigaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi a wani shirin siyasa a ranar Lahadi 03 ga Agusta. Ya bayyana haɗin gwiwar a matsayin “abin da ba zai haifa da mai ido ba.”

Keyamo, yana sharhi kan yanayin siyasa da ke faruwa gabanin babban zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa, ya ce ’yan Najeriya sun saba da dabarun da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ke amfani da su, kuma ba za su sake ruɗewa da waɗannan dabarun da ya kira da tsofaffi ba.

Ya ce, “Su da mu mun san juna sosai. Ba baƙi bane. Waɗannan dabarun da suke amfani da su kamar dabarun ’419’ ne.”

Keyamo ya ƙara da cewa dabarun ADC dabaru ne na ruɗu da ba za su kai ga nasara ba.

Ministan ya kuma zargi ɗaya daga cikin fitattun ’yan adawa da nuna wadata a fili duk da da’awar kare talakawa.

Ya ce, “Ɗaya daga cikinsu yana raina wasa da dukiya, yana tara motoci fiye da 500 a gidansa, amma yana cewa zai ceto ’yan Najeriya.”

Keyamo ya jaddada cewa abin da ya kamata ’yan Najeriya su tambaya shi ne ko gwamnatin Tinubu tana gyara tushen tattalin arziki. A cewarsa, amsar ita ce “eh da ƙarfi.”

Ya ce an samu daidaito a ajiyar kuɗin waje, ƙaruwa a kuɗaɗen shiga na gwamnati, da kuma tsayayyen darajar Naira a matsayin alamun murmurewar tattalin arziki.

“Waɗannan su ne alamun lafiyar tattalin arziki. Sakamakon haka ne za a samu ayyuka da kuɗi a aljihun talakawa,” in ji shi.

Keyamo ya ce jam’iyyar mai mulki tana maraba da ƙalubale daga ’yan adawa domin hakan na taimakawa wajen daidaita turbar aiki. Sai dai ya jaddada cewa alkaluman ƙuri’u ba sa goyon bayan ’yan adawa.

“Tunani cewa haɗin Obi da Atiku zai iya kayar da ƙuri’un mu na mutum miliyan 8.4 da muka samu a 2023 – wannan haɗin ba zai yi tasiri ba,” in ji shi.

Ya bayyana cewa akwai abubuwa uku da suka taimaka wa Obi a zaɓen 2023: addini, ƙabilanci daga Kudu maso Gabas, da goyon bayan matasa da “Obidient”. Amma, a cewarsa, guda biyu daga cikin waɗannan za su rushe idan Obi ya zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a 2027.

“Idan aka ɗora Obi a matsayin mataimaki, ƙungiyar Kiristoci za su ja gefe, su daina shiga harkokin siyasa.

“Kuma fa matar Tinubu fasto ce – wannan yana janyo hankalin Kiristoci. Zai kawar da duk wani ƙididdigar addini da za a yi,” in ji shi.

Keyamo ya kuma yi hasashen cewa yankin Kudu maso Gabas, wanda ya mara wa Obi baya a 2023, zai watsar da shi idan Atiku ya sake fitowa ɗan takarar shugaban ƙasa.

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet