Featured
Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe Tiriliyan 1.5 Wajen Gina Layin Dogo Na Zamani a Birnin Kano

Gwamnatin Tarayya za ta gina layin dogo na zamani a cikin birnin Kano da darajar kusan Naira tiriliyan 1.5, kamar yadda Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi, ya bayyana.
Hon. Bichi, yayin da yake amsa tambayoyi daga ‘yan jarida a Kano, ya ce wannan aikin zai rage matsalolin sufuri a cikin birnin Kano.
Ya ce: “Aikin layin dogon na Kano wanda darajarsa ta kai dala biliyan 1 (kimanin Naira tiriliyan 1.5) nan gaba kadan za a fara aiwatar da shi.
“Wadanda suka yi tafiya zuwa kasashen waje musamman Turai da Asiya sun shaida irin wadannan ayyuka da kuma muhimmancinsu. Wannan aiki zai kara wa tattalin arzikin jihar Kano daraja matuka idan aka kammala shi.”
Hon. Bichi ya ce, sabanin maganganu da ake yadawa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da muhimman ayyuka da dama daga bangaren gine-gine, lafiya, noma, ilimi da tsaro a arewacin Najeriya.
“Abin dariya ne wasu su ce Shugaba Tinubu ba ya sha’awar wannan yankin kasar. Ni ne shugaban kwamitin kasafin kudi, kuma na san irin ayyukan da shugaban ya aiwatar a arewa.
“Dole mu zama masu gaskiya, mu bar son zuciya mu fada gaskiya game da Shugaba Bola Tinubu. Shugaban ya kaddamar da ayyuka masu tarin yawa a arewacin kasar nan.
“Bangaren gine-gine: muna da aikin hanyar Kaduna–Zaria–Kano wanda kusan an kammala. Hanyar Kaduna–Abuja mai tsawon kusan kilomita 400, shugaban ya soke kwangilar farko ya kuma ba wani kamfani daban.
“Sabon kamfanin ya shiga wajen aikin kuma ya yi nasara sosai. Bisa tattaunawata da Ministan Ayyuka, aikin zai kammalu kafin karshen zangon farko na shekara mai zuwa.
“Haka kuma akwai hanyar Kano–Hadejia mai tsawon kilomita 200 wadda an kammala. Akwai kuma hanyar Kano Northern Bypass wadda ta kai wa gwamnati sama da Naira biliyan 250.”