Featured
Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Kafa Sababbin Jami’o’i Masu Zaman Kansu Guda Tara

Gwamnatin Tarayya ta amince da kafa sababbin jami’o’i masu zaman kansu guda tara a fadin Najeriya.
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba 13 ga Agusta, yayin da yake zantawa da ’yan jarida a Fadar Shugaban Kasa, bayan zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a Abuja.
Ya ce, jami’o’in da aka amince da su sun hada da:
Jami’ar Tazkiyah, Jihar Kaduna
Jami’ar Leadership, Abuja
Jami’ar Jimoh Babalola, Jihar Kwara
Jami’ar Bridget, Mbaise, Jihar Imo
Jami’ar Greenland, Jihar Jigawa
Jami’ar JEFAP, Jihar Neja
Jami’ar Azione Verde, Jihar Imo
Jami’ar Unique Open, Jihar Legas
Jami’ar American Open, Jihar Ogun
Alausa ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta gaji bukatun kafa cibiyoyin ilimi sama da 551 da ake jiran amincewa, inda aka bi sabbin tsauraran ka’idojin tantancewa.
Ya kara da cewa da dama daga cikin jami’o’in da aka amince da su suna jiran izinin aiki sama da shekaru shida, inda masu hannun jari suka riga suka gina makarantu da kashe daruruwan biliyoyin naira.
A cewarsa, “Sakamakon rashin ingantacciyar aiki a hukumar NUC, amincewar ta dauki lokaci. Mun aiwatar da sauye-sauye domin saurin tantancewa, kuma amincewar yau ta biyo bayan kammala share wannan jinkirin.”
Ministan ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya ta saka takunkumi kan karbar sababbin bukatun kafa jami’o’i, kwalejojin ilimi, da kwalejojin kimiyya da fasaha, sai wadanda suka cika sabbin ka’idojin aiki.