Featured
NNPP Da APC Sun Lashe Zabukan Cike-Gurbi a Jihar Kano

Jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar ta lashe zaɓen cike gurbi na ɗanmajalisar jiha a mazaɓar Bagwai da Shanono.
A gefe guda kuma, APC mai adawa ce ta lashe ƙarashen zaɓen ɗanamajlisa da aka yi a ƙaramar hukumar Gari da Tsanyawa.
Da yake sanar da sakamakon a cikin daren da ya gabata, baturen zaɓe Farfesa Hassan Adamu Shitu ya sanar da Ali Hassan Kiyawa na NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen na Bagwai da Shanono da ƙuri’a 16,198.
Sakamakon ya nuna cewa ya doke ɗantakatarar APC mai adawa Ahmad Muhammad Kadamu, wanda ya zo na biyu da ƙuri’a 5,347.
A gefe guda kuma, APC mai adawa ce ta lashe ƙarashen zaɓen ɗanamajlisa da aka yi a ƙaramar hukumar Gari da Tsanyawa.
Baturen zaɓen INEC Farfesa Muhammad Waziri daga jamiʼar Bayero ne ya sanar da hakan da ƙarfe 6:10am na ranar Lahadi 17-08-2025. Inda ya bayyana dan takarar APC a matsayin wanda ya samu kuri’a 31472, yayin da dan takarar NNPP ya samu kuria 27931.