Featured
Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Allah-wadai Da Ministan Isra’ila

Ofishin kare haƙƙin ɗan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Talata 19 ga Agusta, ya yi Allah-wadai da wani ministan Isra’ila mai ra’ayin rikau saboda yi wa wani ɗan fursunan Falasɗinu izgili a cikin ɗakinsa tare da yada bidiyon a kafafen sada zumunta.
Ministan Tsaron Cikin Gida na Isra’ila, Itamar Ben Gvir, ya wallafa wani bidiyo a makon da ya gabata inda aka ganshi a fusace yana magana da Marwan Barghouti, ɗaya daga cikin sanannun fursunonin Falasɗinu da Isra’ila ke tsarewa.
Kakakin ofishin kare haƙƙin ɗan adam na MDD, Thameen Al-Kheetan, ya bayyana cewa wannan bidiyo bai kamata ba, yana mai cewa: “Halin da ministan ya nuna da kuma wallafa wannan bidiyo na nufin cin mutuncin Barghouti ne.”
Barghouti, wanda yanzu ya shiga shekaru sittin, an yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai a shekarar 2004 bisa tuhume-tuhumen kisan kai.
Isra’ila na kallon shi a matsayin ɗan ta’adda, amma a wajen Falasɗinu kuwa, shi ne yake kan gaba a jerin shugabannin da suka fi shahara, inda wasu ma ke kiran shi da “Mandela na Falasɗinu.”
Al-Kheetan ya jaddada cewa: “Dokokin ƙasa da ƙasa suna wajabta a rika kula da duk wanda aka tsare cikin adalci da mutunci, tare da tabbatar da kariya da girmama haƙƙinsu.”
Ya kuma yi gargadi cewa abinda ministan ya aikata “na iya haifar da tashin hankali kan fursunonin Falasɗinu” tare da buɗe ƙofa ga cin zarafi a gidajen yari na Isra’ila.