Featured
Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Buƙaci A Gaggauta Kawo Ƙarshen Yaƙin Gaza
Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya sake sabunta kiran gaggawa na tsagaita wuta a Gaza, bayan da Isra’ila ta sanar da fara kai farmaki domin ƙwace birnin Gaza.
Mista Guterres ya ce, wajibi ne a guji kashe-kashe da kuma lalata rayuka da dukiyoyi da wannan farmaki zai iya haifarwa.
Rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewa ta kaddamar da matakin farko na farmakin a Gaza, inda Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya bayyana shi a matsayin yunkuri na ƙwace abin da ya kira “wurin ƙarshe” a Gaza.
A cewar jami’ai a Gaza, dubban Falasɗinawa sun fara tserewa daga birnin da ya ƙunshi fiye da miliyan ɗaya na mazauna.
