Addini
Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Juma’a A Matsayin Ranar Hutun Maulidi

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a, 5 ga Satumba, 2025, a matsayin hutu domin bikin Maulidin Annabi Muhammadu (SAW). Wannan na cikin wata sanarwa da Sakataran Dindindin na Ma’aikatar Cikin Gida, Dakta Magdalene Ajani ta fitar a madadin Ministan Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, inda ta taya musulmi murnar wannan rana mai albarka.
Gwamnati ta yi kira ga musulmi da su yi koyi da kyawawan dabi’un Annabi Muhammadu (SAW) na zaman lafiya, soyayya, tawali’u, hakuri da jin kai. Haka kuma ta bukaci ’yan Najeriya na addinai daban-daban da su yi amfani da wannan dama wajen rokon zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a kasa tare da mara wa gwamnati baya wajen hadin kan kasa da ci gaba mai dorewa.
Ministan Cikin Gida ya taya musulmi murnar bikin Maulidi mai cike da farin ciki da kwanciyar hankali. Ya ce wannan biki wata dama ce ta kara karfafa zumunci, tare da yin koyi da koyarwar Annabi (SAW) na hidima ga al’umma ba tare da son kai ba.