Connect with us

Featured

Kungiyar Masu Dakon Man Fetir Da Iskar Gas Sun Janye Yajin Aiki Bayan Ƙulla Yarjejeniya Da Matatar Dangote

Kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (NUPENG) ta dakatar da yajin aikin kwana biyu bayan wani taro da gwamnatin tarayya da kuma kamfanin Dangote. Yajin aikin ya janyo rufe gidajen mai a sassa daban-daban na ƙasar, inda jama’a suka fuskanci matsalolin samun man fetur.

A cikin yarjejeniyar da aka cimma, matatar mai ta Dangote ta amince da bai wa ma’aikatanta damar shiga ƙungiyoyin kwadago bisa tsarin doka. An yanke hukuncin cewa za a kammala tsarin rajista da haɗa ma’aikata cikin ƙungiya tsakanin 9 zuwa 22 ga Satumba, 2025. An kuma tabbatar da cewa babu wani ma’aikaci da za a yi wa ramuwar gayya saboda yajin aikin.

Yarjejeniyar ta samu sa hannun wakilan Dangote, shugabancin NUPENG, jami’an hukumar kula da man fetur (NMDPRA), ma’aikatar ƙwadago, da kuma manyan ƙungiyoyin kwadago na ƙasa (NLC da TUC). Wannan ya sa NUPENG ta dakatar da yajin aikin da gaggawa.

Sai dai kafin dakatarwar, yajin aikin ya riga ya janyo rufe gidajen mai a jihohi da dama kamar Kaduna da Cross River, sannan an samu hauhawar farashin mai a wasu wurare kamar Sokoto da Enugu. Haka kuma, mutane da dama sun shiga tsoron karancin man fetur inda aka ga karuwar sayen mai a jihohin Legas da Ogun.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet