Featured
INEC Ta Zargi Jam’iyyun Siyasa Da Fara Yaƙin Neman Zaɓe Tun Lokaci Bai Yi Ba
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta nuna rashin jin daɗi kan yaƙin neman zaɓe da wasu jam’iyyun siyasa da ‘yan takara ke gudanarwa tun kafin lokacin da doka ta tanada, a shirye-shiryen zaɓen 2027.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja, inda ya ce babban ƙalubalen hukumar shi ne giɓin da ke cikin dokar zaɓe. Ya tunatar da cewa dokar zaɓe ta 2022 ta kayyade fara yaƙin neman zaɓe kwanaki 150 kafin zaɓe, amma babu wani hukunci da aka tsara ga masu karya wannan tanadi.
Yakubu ya ce wannan gibin ya sa hukumar ba ta da ikon sa ido sosai kan kuɗaɗen da jam’iyyu da ‘yan takara ke kashewa kafin lokacin yaƙin neman zaɓe. A cewarsa, hakan na iya shafar tsarin gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci.
