Connect with us

Featured

NDLEA Ta Kama Tabar Wiwi Cikin Wata Mota Da Ta Yi Hatsari A Kano

Hukumar NDLEA reshen Kano ta kama tabar wiwi mai nauyin kilo 112, bayan wani hatsarin mota da ya auku a Gadar Tamburawa, kan titin Zariya–Kano. Hukumar ta ce jami’anta da ke sintiri sun isa wurin ne bayan jin karar karo tsakanin motar Golf da wata babbar mota.

A cewar mai magana da yawun hukumar, Sadiq Muhammad-Maigatari, jami’an sun ceto direba da fasinja daga motar Golf, inda fasinjan ya yi ƙoƙarin tserewa amma aka cafke shi. Bincike da aka gudanar a cikin motar ya sa aka gano buhunan tabar wiwi guda 150.

Direban da ke jinya ya amsa cewa shi wakilin mai kayan ne, kuma ya taba kai irin wannan kaya a baya, ciki da wajen Kano. Ya kuma bayyana cewa ya yi amfani da hanyar “one way” domin kaucewa shingen NDLEA, lamarin da ya haddasa hatsarin.

Hukumar ta tabbatar da cewa za ta gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kotu, tare da yabawa jami’an da suka gudanar da aikin cikin kwarewa. Ta kuma ja kunnen jama’a da su guji safarar miyagun ƙwayoyi, tare da neman a rika sanar da hukumar duk wani motsi mai kama da na miyagun kwayoyi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet