Featured
Matsalar Hauhawar Farashin Kayayyaki Ta Kusa Zama Tarihi a Najeriya – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa hauhawar farashin kaya zai sauka ƙasa sosai har ya kai ɗigo ɗaya nan gaba kaɗan. Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tattalin arziƙi, Tope Fasua, ne ya bayyana haka a shirin The Morning Brief na Channels TV, inda ya ce sauƙin farashin zai taimaka wajen ragewa al’umma tsadar rayuwa.
A cewar Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), hauhawar farashin kaya ya ragu daga kashi 21.88% a watan Yuli 2025 zuwa kashi 20.12% a watan Agusta 2025 – raguwa ta kashi 1.76%. NBS ta ce wannan na nuni da cewa farashin kaya na ci gaba da sauka, duk da cewa har yanzu ana jin zafi a wasu fannoni.
Fasua ya ce raguwar hauhawar farashin kaya na faruwa ne sakamakon sabbin matakai da aka ɗauka, musamman wajen sabunta tsarin ƙididdiga da kuma daidaiton musayar kudin waje. Ya kuma bayyana cewa farashin abinci ya fara sauka, kuma a wannan shekara ba a samu tashin farashin tumatir kamar yadda aka saba ba.
Mai ba Shugaban Ƙasa shawarar ya ƙara da cewa, kamar yadda Ghana da Pakistan suka fuskanci hauhawar farashin kaya mai tsanani kafin ya sauka, haka ma hauhawar farashin zai zama tarihi a Najeriya. Ya ce darajar Naira na ƙara ƙarfi yayin da farashin man fetur a kasuwannin duniya ke ƙaruwa, abin da ke taimakawa wajen rage tashin farashin kaya a ƙasar.