Featured
Shugaba Tinubu Zai Shiga Tarihi a Matsayin Wanda Ya Farfaɗo Da Tattalin Arzikin Najeriya – Yakubu Dogara

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ya bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda zai shahara a tarihi a matsayin babban wanda sauya tattalin arzikin Najeriya. Dogara ya yaba wa manyan sauye-sauyen haraji da Shugaban kasa ya kaddamar, yana mai kiran su mafi girma da aka taba yi a tsarin kuɗin shiga na kasa cikin shekaru da dama.
Dogara, wanda ya gabatar da jawabi a babban taron “Distinguished Parliamentarian Lecture” na farko da aka shirya a Majalisar Wakilai, ya bayyana cewa Tinubu ya gaji tattalin arziki mai rauni, cike da matsaloli kamar cin gajiyar musayar kudade da wasu ‘yan tsiraru ke yi, yawaitar buga kuɗi da kuma sayar da man fetur gaba da gaba domin ɗaukar rance daga kasashen waje.
Ya ce sauye-sauyen sun haɗa dokoki 16 na haraji zuwa manyan dokoki guda hudu, ciki har da “Nigeria Tax Act 2025” da “Nigeria Revenue Service (Establishment) Act 2025,” waɗanda za su fara aiki a watan Janairu 2026. Sabbin dokokin za su sauƙaƙa tsarin haraji, fadada hanyar tara kudaden shiga, da kare talakawa ta hanyar ware ƴan kananan kamfanoni da ma’aikata masu ƙaramin albashi daga biyan haraji.