Connect with us

Featured

Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Darasin Tarihi Cikin Tsarin Koyarwa a Makarantun Firamare da Sakandare

Gwamnatin Tarayya ta mayar da darasin Tarihin Najeriya cikin kundin karatun makarantu na firamare da sakandare a matakin farko bayan kusan shekaru da dama da aka cire shi. Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin ta na X a ranar Laraba 17 ga Satumba, inda ta bayyana cewa darasin Tarihi ya zama dole ga dalibai domin karfafa kishin kasa, hadin kai da nagartar zama ‘yan kasa nagari.

Sanarwar ta ce wannan shi ne karo na farko cikin shekaru da dama da za a koyar da Tarihi daga ajin Primary 1 har zuwa JSS3 ba tare da yankewa ba, yayin da daliban sakandare daga SSS1 zuwa SSS3 za su fara sabon darasin Civic and Heritage Studies, wanda aka hade Tarihi da Darasin Zamantakewa.

A cikin sabon tsarin, yara daga Primary 1 zuwa 6 za su san asalin Najeriya, jarumai, shugabanni, al’adu, addinai, siyasa, tattalin arziki, mulkin mallaka da tafiyar kasar bayan samun ‘yancin kai. A JSS1 zuwa JSS3 kuwa, za a koyar da su game da dauloli, kasuwanci, hulda da Turawa, hadewar kasa, samun ‘yancin kai da dimokuradiyya tare da darussan zamantakewa.

Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa an riga an fitar da sabon kundin karatun, za a horas da malamai, a samar da kayan koyarwa da kuma karfafa sa-ido. Darasin Tarihi dai an cire shi daga kundin karatun makarantu a shekarar 2009/2010 sakamakon dalilan karancin malamai da rashin sha’awar dalibai, kafin gwamnatin tarayya ta fara shirin dawo da shi daga 2017 zuwa yanzu.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet