Connect with us

Featured

Gwamnatin Tarayya Ta Raba Naira Biliyan 330 Ga Talakawa a Faɗin Najeriya Domin Rage Radadi – Ministan Kuɗi

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta raba Naira biliyan 330 ga talakawa da marasa galihu a fadin kasar nan a matsayin tallafin rage radadin cire tallafin man fetur da sauyin kudin musayar waje. Ministan Kudi kuma Koodinatan Tattalin Arziki, Mista Wale Edun, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Abuja, inda ya ce an gudanar da shirin ne ta hannun Hukumar National Social Safety-Net Coordinating Office (NASSCO).

Ministan ya ce an tantance gidaje miliyan 19.7 masu fama da talauci a kundin rajistar kasa, wanda hakan ya shafi sama da mutane miliyan 70. Daga cikin wannan adadi, gidaje miliyan 15 ne ake su ka amfana, kuma zuwa yanzu gidaje miliyan 8.5 sun riga sun karɓi akalla Naira 25,000, wasu kuma sun karɓa sau biyu ko sau uku.

Ya kara da cewa sauran gidaje miliyan 7 za su karɓi nasu kudin kafin karshen shekara, yayin da gwamnati ta bullo da tsarin saka kudin tallafi a kasafin kudi na kowace shekara don tabbatar da dorewar shirin. An kuma tabbatar da sahihancin masu cin gajiyar shirin ta hanyar amfani da Lambar Shaidar Kasa (NIN) da kuma biyan kudi kai tsaye ta asusun banki ko wayar hannu.

A nata bangaren, Koodinetar NASSCO, Hajiya Funmi Olotu, ta ce tsarin karɓar kudin kai tsaye daga banki ko wayar hannu ya maye gurbin tsohon tsarin karɓar kudi a hannu, domin tabbatar da gaskiya da bin doka, abin da ya sa wasu gidaje suka karɓi kudin sau daya ko fiye da haka tun bayan fara shirin.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet