Connect with us

Featured

Shugaba Tinubu Ya Sha Alwashin Ci gaba Da Aiwatar Da Manufofin Marigayii Muhammadu Buhari

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci iyalan marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a Kaduna, inda ya jajanta musu tare da tabbatar da cewa zai ci gaba da aiwatar da kyawawan manufofin mahaifinsu.

Mai ɗakin Marigayi ShugabanBuhari, Aisha Buhari, ɗanta Yusuf, da sauran ‘yan uwa da abokan marigayin su ne su ka tarbi shugaba Tinubu yayin ziyarar, ya ce Buhari ya bar alamar gaskiya, jajircewa da kishin ƙasa, kuma gwamnati za ta ci gaba a kan wannan tafarki.

Aisha Buhari ta gode wa Shugaba Tinubu bisa wannan ziyara, tana mai cewa ta kawo musu kwarin gwiwa da kwantar da hankali. Ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi koyi da gaskiya, adalci, da jajircewar da mijinta ya yi fice da su. Ta yi addu’a ga Shugaba Tinubu da kuma ƙasar Najeriya domin zaman lafiya da haɗin kai su dore.

Shugaban Ƙasa ya samu rakiyar manyan jami’an gwamnati ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da wasu gwamnonin jihohi. Wannan ziyara ta nuna alamar haɗin kai da ci gaba da girmama tsohon shugaba da aikinsa ga ƙasa.

Tun kafin haka Shugaba Tinubu ya halarci ɗaurin aure na Nasirudeen, ɗan Sanata Abdulaziz Yari, da Safiyya Shehu Idris a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna. Ya yabawa iyalan amarya da ango bisa riƙon al’adun kirki tare da yi musu nasiha kan gina zaman aure da imani, soyayya da girmama juna. An yi addu’o’i na alheri ga Shugaban Ƙasa da ƙasa baki ɗaya daga manyan malaman addini.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet