Connect with us

Featured

Ƴan Sanda Za Su Fara Hukunta Motocin Da Aka Sanyawa Baƙin Gilashi Ba Tare da Lasisi ba Daga 2 Ga Oktoba

Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar Jigawa ta sanar da cewa daga ranar 2 ga Oktoba, 2025 za a fara aiwatar da dokar hukunta motocin da aka sanya musu baƙin gilashi ba tare da izini ba a fadin ƙasar. Kakakin rundunar, SP Shi’isu Adam, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse. Ya ce yanzu haka ana ci gaba da yin rijista ta yanar gizo ta shafin possap.gov.ng, inda masu niyyar neman lasisi za su bi matakai cikin sauƙi.

A cewar sanarwar, duk wanda zai nema sai ya kirkiro asusu da NIN, BVN ko TIN, sannan ya tabbatar da asusun ta imel, ya shiga shafin ya zaɓi sabis na “Tinted Glass Permit” ya kuma loda bayanan motarsa da takardun da suka dace. SP Adam ya ja hankalin jama’a su tabbatar da daidaiton bayanai kafin su mika bukata da biyan kuɗi don saurin amincewa.

Ya ƙara da cewa za a shirya lokacin duba mota da ɗaukar bayanan yatsun hannu (biometric capturing) a sashen leƙen asiri na rundunar ‘yan sanda. Musamman a Jigawa, ya ce za a yi wannan aikin kyauta a Sashen Leƙen Asiri na hedkwatar ‘yan sanda, Dutse.

SP Adam ya gargadi jama’a kada su bi mutane marasa izini da ke amfani da tsarin don yaudara. Ya ce wannan shiri zai ƙara gaskiya, tsaro da bin doka a hanya. Rundunar ta kuma bukaci haɗin kan jama’a don kauce wa matsaloli da kuma kare direbobi daga kamawa kan gilashin mota marar lasisi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xgrandpashabetgrandpashabetpusulabetvdcasinograndpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetcasibom girişcasinolevantcasinolevantmatbetholiganbetholiganbet girişcasibomcasibom girişjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetcasibomcasinolevantgrandpashabetcasibomsekabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet