Connect with us

Featured

Ramaphosa Zai Halarci Taron Majalisar Ɗinkin Duniya Kan Rikicin Isra’ila Da Falasɗinu

Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, zai shiga taron manyan jami’ai da za a gudanar a hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) a birnin New York a ranar Litinin 22 ga Satumba, domin tattaunawa kan tsarin samar da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falasɗinu. Gidan talabijin na ƙasar, SABC, ya ruwaito cewa taron na da nufin inganta goyon bayan ƙasashen duniya ga tsarin kafa ƙasar Falasɗinu.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, tare da Yariman Saudiyya, Mohammed Bin Salman, ne za su jagoranci taron, inda za a tattauna dabarun da za su ƙara ƙarfafa goyon bayan ƙasashe da dama wajen kafa tsarin ƙasar biyu. Hakan na zuwa ne kwanaki bayan wasu ƙasashen Yammacin Turai, ciki har da Birtaniya, su ka amince da kafa ƙasar Falasɗinu a hukumance.

Afirka ta Kudu ta daɗe tana mara baya ga kafa ƙasar Falasɗinu, inda ta kai Isra’ila gaban Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Ƙasa da Ƙasa (ICJ) bara, bisa zargin aikata kisan ƙare dangi a Gaza. Wannan mataki ya ƙara bayyana matsayin ƙasar kan batun Falasɗinu da Isra’ila a idon duniya.

Ofishin shugaban ƙasar ya bayyana cewa Ramaphosa zai yi jawabi a gaban MDD gobe, inda zai jaddada buƙatar haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa domin samar da zaman lafiya ta hanyar tattaunawa, da kuma ƙarfafa kare haƙƙin ɗan adam ga kowa ba tare da nuna bambanci ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet