Connect with us

Featured

Kungiyar HEDA Ta Bukaci Gwamnati Ta Bayyana Sunayen Waɗanda Suka Amfana da Tallafin Naira Biliyan 330

Kungiyar HEDA Resource Centre ta bukaci gwamnatin tarayya ta wallafa cikakken jerin sunayen wadanda suka amfana da Naira biliyan 330 da aka raba wa talakawa ta hannun Hukumar National Social Safety-net Coordinating Office (NASSCO). Kungiyar ta ce wannan ya zama dole ne domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen gudanar da kudaden jama’a.

Bukatar HEDA na zuwa ne bayan ministan kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Wale Edun, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta fara rabon kudaden tallafi daga bashin Dala miliyan 800 na Bankin Duniya domin rage radadin matsin tattalin arziki da cire tallafin mai ya haifar.

Shugaban HEDA, Olanrewaju Suraju, ya bayyana cewa ikirarin gwamnatin tarayya na biyan N330bn ya fi “haifar da tambayoyi fiye da amsoshi”, yana mai cewa ’yan Najeriya na da hakkin sanin yadda aka zabi wadanda suka amfana da kuma yawan kudaden da kowanne ya samu. Ya kara da cewa rashin bayyanawa zai iya sa tsarin ya zama hanyar cin hanci.

Kungiyar ta kuma yi kira da a sanya dukkan kasafin kudaden jin kai a nan gaba karkashin kulawa da kungiyoyin farar hula, kafafen yada labarai, da jama’a, domin a tabbatar cewa an yi amfani da kudaden wajen taimakon masu bukata na gaskiya, ba ‘yan boko ko sunayen bogi ba.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet