Connect with us

Featured

Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Shigar da Sojoji Cikin Tsarin Inshorar Lafiya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyar ta na haɗa duka jami’an soji da iyalansu cikin tsarin National Health Insurance Authority (NHIA) domin tabbatar da cikakkiyar kula da lafiyarsu Ministan Tsaron Ƙasa, Bello Matawalle, ya bayyana hakan a Abuja yayin bikin cika shekara 20 da haɗin gwiwar Ministry of Defence Health Implementation Programme da Walter Reed Army Institute of Research Africa. Ya ce shirin zai ƙara ƙarfin tsarin kiwon lafiyar tsaro na ƙasa tare da tabbatar da sojoji da iyalansu suna amfana da kariya irin ta sauran ‘yan ƙasa.

Matawalle ya jaddada cewa lafiyar jami’an tsaro na da alaƙa kai tsaye da tsaron ƙasa, inda ya ce kulawa da kiwon lafiya da kariya daga cututtuka na taimakawa wajen tabbatar da shirin sojoji na ci gaba da kare ƙasar. Ya ce haɗin gwiwar tsaron lafiya da aka kafa tun shekaru 20 da suka gabata ta amfanar da sama da rabin miliyan, ciki har da sojoji da fararen hula, ta gina cibiyoyi, kuma ta ƙara wa jama’a amincewa da kulawar lafiyar da rundunar soji ke jagoranta.

Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa haɗa jami’an tsaro cikin NHIA muhimmiyar hanya ce da za ta taimaka musu su kasance cikin koshin lafiya don kare ƙasar. Ya bayyana haɗin gwiwar da Walter Reed a matsayin abin koyi na haɗin kan ƙasa da ƙasa da ya inganta cibiyoyin kiwon lafiyar sojoji 32 a faɗin ƙasar tare da kawo gagarumar gudummawa ga al’umma wajen yaki da HIV, COVID-19 da sauran cututtuka.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet