Featured
Ƴan Najeriya Sama Da Miliyan 6.2 Sun Kammala Rijistar Katin Zaɓe Ta Intanet – INEC
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa sama da ‘yan Najeriya miliyan 6.2 ne suka kammala rijistar zaɓe ta intanet a mako na shida na shirin Rijistar Zaɓe (CVR). A cewar bayanan da hukumar ta fitar a shafinta na X da kuma shafin yanar gizo na hukumar, adadin ya kai 6,232,673 daga ranar 22 zuwa 28 ga Satumba, 2025.
Daga cikin wannan adadi, mata sun fi yawa, inda adadin su ya kai 3,250,338 wanda ya kai kashi 52.15 cikin ɗari, yayin da maza suka kasance 2,982,335 kashi 47.85 cikin ɗari. Matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 34 sun mamaye shirin da mutum 4,230,715, yayin da ɗalibai suka kai 1,565,824, sannan kuma mutane masu nakasa sun kai 137,865.
INEC ta ƙara bayyana cewa a mako na biyar (22 zuwa 26 ga Satumba, 2025) mutane 1,004,132 ne suka kammala rijistarsu gaba ɗaya – ciki har da 537,743 da suka kammala ta intanet, da kuma 466,389 da suka kammala a ofisoshin hukumar.
A cikin waɗanda suka kammala rijista a mako na biyar, mata sun fi yawa da 555,077 kashi 55.28 cikin ɗari, maza kuwa 449,055 kashi 44.72 cikin ɗari. Matasa sun kai 742,379 daga cikin jimillar, ɗalibai 354,406, yayin da masu nakasa suka kai 13,987.
