Fashion
Gwamnatin Tarayya Ta Soke Gudanar Da Fareti a Ranar Samun Ƴancin Kai

Gwamnatin tarayya ta bayyana soke faretin da aka shirya gudanarwa domin murnar zagayowar cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai, a ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025. Sanarwar ta fito ne daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya a ranar Litinin.
A cewar sanarwar, wannan mataki ba zai rage darajar muhimmancin ranar ba, kasancewar ita ce rana ta tarihi ga ‘yan Najeriya baki ɗaya. Gwamnati ta kuma nemi afuwar al’umma kan wannan canjin da aka yi a shirin bukukuwan.
Duk da soke faretin, sauran shirye-shiryen da aka tsara domin bikin za su ci gaba kamar yadda aka tsara tun farko. Wannan ya haɗa da jawabin shugaban ƙasa ga al’umma, bukukuwan al’adu da kuma wasu taruka na musamman.
Hakan na zuwa ne yayin da gwamnatin tarayya ta jaddada bukatar gudanar da bikin cike da natsuwa da kuma nuna haɗin kai tsakanin al’umma. An kuma yi kira ga ‘yan ƙasa da su ci gaba da tunawa da darajar ranar da ta kafa harsashin dimokuraɗiyya da ‘yancin kai a ƙasar.