Featured
Gwamna Abba Ya Buƙaci Shugaban Ƙasa Ya Sauke Kwamishinan Ƴan Sandan Kano

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya janye jami’ansa daga jerin gwanon taron bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a Kano. Yusuf ya ce wannan mataki ya zama abin kunya ga jihar da kuma nuna raini ga al’ummar Kano a ranar tarihi irin ta ƙasa.
A jawabinsa yayin bikin ranar Talata, gwamnan ya yi zargin cewa kwamishinan ‘yan sandan ya nuna halin son rai da siyasa, wanda ya kira da “ba daidai ba” da kuma saba wa tsarin doka. Ya ce matsayin kwamishinan ya haifar da rashin daɗi ga jama’a, musamman ganin cewa Kano na cikin kwanciyar hankali, kuma mutane sun fito ne domin bikin cikar ƙasa shekaru 65.
Yusuf ya jaddada cewa matsayin kwamishinan ya sabawa matsayin sa na babban jami’in tsaro na jihar, inda ya bayyana cewa janyewar ‘yan sanda a daidai lokacin da ake sa ran hadin kai da tsaro ya kamata, ya nuna rashin kishin ƙasa. “Wannan abu ne da ba za mu lamunta ba a matsayinmu na al’umma da ke son zaman lafiya,” in ji shi.
Sai dai kwamishinan ‘yan sandan, Ibrahim Adamu Bakori, da aka tuntuba kan lamarin, ya ce yana cikin wani gaisuwar ta’aziyya ne, yana mai ƙara da cewa zai kira daga baya. Duk da haka, gwamnan ya gode wa sauran hukumomin tsaro da suka halarci bikin, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da goyon bayan ci gaba da zaman lafiya da haɗin kai a jihar.