Connect with us

Featured

Gwamnatin Tarayya Za Ta Buɗe Kwalejin Fasaha Ta Bayelsa Bayan Shafe Watanni a Kulle

Gwamnatin Tarayya ta sasanta rikicin ma’aikata da ya daɗe yana addabar Federal Polytechnic, Ekowe, da ke jihar Bayelsa, wanda ya jawo rufe makarantar tun daga 11 ga Yuli. Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya kira bangarorin da abin ya shafa a taron sulhu a Abuja ranar 29 ga Satumba, inda aka cimma matsaya cewa makarantar za ta ci gaba da aiki daga ranar 6 ga Oktoba.

A taron, shugabanni da sakatarorin ƙungiyoyi uku na ma’aikata (NASU, SSANIP da ASUP), tare da shugaban kwamitin gudanarwa na makarantar, sun bayyana matsayinsu. Bayan tattaunawa, ministan ya umarci kwamitin gudanarwa ya kafa sabuwar kwamiti domin bincikar korafe-korafe da ake yi wa Dr. Agbabiaka Lukman, tare da bayar da rahoto a cikin makonni uku.

Rikicin ya samo asali ne daga ƙarar da Rector ya kai ƙungiyoyin ma’aikata a kotu kan batutuwan kwadago, alhali dokar Polytechnic ta tanadi cewa irin waɗannan matsaloli na karkashin hurumin kwamitin gudanarwa. Kungiyoyin sun ce dole ne a dakatar da Rector kafin ci gaba da aiki don samun zaman lafiya a makarantar.

Tun da farko, ma’aikata sun zargi cewa an dakatar da wani zama na kwamitin gudanarwa bisa hujjar rashin tsaro, duk da cewa babu wata barazana a Bayelsa a lokacin. Sai dai bayan shiga tsakani na ministan, an cimma matsaya cewa makarantar ta buɗe, yayin da kwamitin bincike zai zurfafa cikin rahoton korafe-korafen da ake yi wa Rector.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvmarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasibomcasibomjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasibomgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet