Connect with us

Featured

Ranar Ƴancin Kai : Jawabin Tinubu Duk Hasashe Ne Babu Gaskiya – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya mayar da martani ga jawabin bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi. Atiku ya ce jawabin shugaban ƙasa cike yake da ƙarya da hasashe mara tushe, inda ya kwatanta Najeriya da “tukunyar da ta fashe, wadda ba za ta iya dafa doya ba, alhali talakawa na ci gaba da jin yunwa.”

A cewar Atiku, duk da cewa Tinubu ya yi ta yabon ci gaba a fannin ilimi, hakikanin gaskiya shi ne, dalibai da dama har yanzu na karatu a ƙasa, ba tare da kujeru ko kayan rubutu ba, yayin da malamai ke barin ajujuwa saboda rashin albashi mai inganci. Haka kuma, Atiku ya ce ikirarin ƙarin asibitoci ya zama na banza ne, domin marasa lafiya har yanzu sukan je da kyandir, magunguna da kayan aiki kafin a fara musu jinya.

Game da tattalin arziki kuwa, Atiku ya bayyana cewa al’ummar ƙasar sun fi jin radadin hauhawar farashin kayayyakiba yanzu, tsadar sufuri, da yunwar da ta addabi gidaje fiye da kowanne lokaci. Ya ce gwamnati na ta magana kan “’ya’yan garambawul,” alhali abin da ‘yan Najeriya ke gani shi ne wuya da talauci. A fannin tsaro kuma, duk da cewa Tinubu ya yi yabon rundunar soji, mutane har yanzu na biyan kudin fansa ga ‘yan ta’adda, suna kwana da tsoro, kuma ƙauyuka na ci gaba da binne gawawwaki.

Atiku ya jaddada cewa Najeriya ta jure wahalhalu da dama cikin shekaru 65 da suka gabata, amma hakan bai nufin cewa jama’a sun gamsu da halin da ake ciki ba. Ya ce talauci da yunwa sun mamaye ƙasa, matasa sun rasa aikin yi, kuma gwamnatin Tinubu ta kasa samar da dama mai inganci. “Shugaba ba zai iya cewa an dafa doya ba, idan tukunyar ta fashe,” in ji Atiku, yana mai cewa abubuwan da Tinubu ke furtawa a jawabi ba su da tushe a rayuwar talakawa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet