Connect with us

Featured

Girgizar Ƙasa ta Hallaka Mutum 72 a Philippines

Girgizar ƙasa mai ƙarfi da ta afku a tsakiyar ƙasar Philippines ta yi ajalin mutum 72, tare da raunata sama da 290 da kuma raba dubban jama’a da gidajensu. Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasar ta tabbatar da cewa babu wanda ake nema a halin yanzu, inda ta umarci wasu rukunin ceto a lardin Cebu da su fara ja da baya daga aikin bincike.

Rahotanni sun nuna cewa sama da gidaje 600 sun rushe a arewacin Cebu, inda mutane da dama suka kwana a tituna saboda fargabar ƙarin girgizar da ke ci gaba da afkuwa a yankin. Gwamnan lardin Cebu, Pamela Baricuatro, ta yi kira ga gwamnati da kungiyoyin agaji da su hanzarta kawo ruwan sha, abinci, kayayyakin sawa da kuma mafaka ga dubban jama’ar da bala’in ya rutsa da su.

Shugaban ƙasar Ferdinand Marcos ya ziyarci yankin da abin ya shafa a ranar Alhamis 02 ga Oktoba, inda ya duba barnar da ta shafi gidajen da aka gina tun bayan mummunar guguwar Haiyan ta 2013. Rahotanni sun ce wasu gidaje daga cikin wannan shiri sun ruguje, inda aka ciro gawarwakin mutane takwas daga cikinsu.

Mutanen yankin sun bayyana matsalolin da suke fuskanta, musamman rashin ruwa da wutar lantarki, yayin da marasa lafiya ke karɓar magani a cikin tanti a wajen asibitin lardin Cebu da ya lalace. Fiye da mutane 110,000 a cikin al’ummomi 42 ake buƙatar taimako don su farfaɗo daga wannan masifa, wacce ta sake tunasar da jama’a cewa Philippines na daga cikin yankunan da ke cikin haɗarin girgizar ƙasa akai-akai saboda kasancewarta a “Zoben Wuta” na Pasifik.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet