Featured
Akwai Yiwuwar Mu Shiga Sabon Yajin Aiki – PENGASSAN

Ƙungiyar ma’aikatan manyan jami’an mai da iskar gas a Najeriya (PENGASSAN) ta bayyana cewa ba ta sanya hannu kan yarjejeniyar da ta kawo ƙarshen yajin aikin da ta kaddamar a kan kamfanin Dangote Refinery ba. Kungiyar ta ce dakatar da yajin aikin a ranar Laraba 01 ga Oktoba, bayan shiga tsakani da gwamnatin tarayya ta yi, ba yana nufin matsalolin da suka sa ta shiga yajin aiki sun kau ba.
Shugaban PENGASSAN, Festus Osifo, ya bayyana a taron manema labarai cewa akwai “matsaloli da dama” a cikin sanarwar da Ministan Kwadago, Muhammadu Dingyadi, ya gabatar a matsayin mai sasanta rikicin. Ya ce kungiyarsu ta ki sanya hannu saboda akwai abubuwan da ba su dace ba, inda ya kara da cewa abin da suka fi bai wa muhimmanci shi ne dawo da ma’aikatan da aka kora fiye da 800.
Osifo ya soki zargin da kamfanin Dangote ya yi cewa korarrun ma’aikatan sun yi ƙoƙarin lalata tattalin arziki, yana mai cewa hakan ba gaskiya ba ne kuma zai iya zama tabo a rayuwar waɗanda aka kora. Ya jaddada cewa matsayar PENGASSAN ita ce a gaggauta mayar da su bakin aiki domin kare ‘yancin ma’aikata na shiga ƙungiya.
Ya gargadi kamfanin Dangote cewa idan bai yi abin da ya dace ba, za su iya sake komawa yajin aiki ba tare da wani gargadi ba. “Mun sha gwagwarmaya tsawon shekaru 50 kafin refinery ta zo, kuma ba za mu gaji da kare ma’aikata ba,” in ji shi.