Connect with us

Featured

Kamfanin NNPC Da Sauran Ma’aikatan PENGASSAN Sun Tsunduma Yajin Aiki a Fadin Najeriya

Rikicin man fetur ya dauki sabon salo a Najeriya, bayan an wayi gari a yau Litinin 29 ga Satumba, 2025, inda Kungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur (PENGASSAN) ta fara yajin aiki na kasa baki daya. Yajin aikin ya durkusar da ayyuka a manyan hukumomin kula da harkokin man fetur da gas na kasa, ciki har da NNPC Limited, Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission (NUPRC), da kuma Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA). Wakilin KAKAKI24 ya gano cewa ko kofar shiga hedikwatar NUPRC a Abuja an kulle ta tsaf, inda jami’an tsaro suka tabbatar da cewa babu wani ma’aikaci da aka bari ya shiga.

Kungiyar PENGASSAN ta ce ta dauki matakin ne saboda korar ma’aikata 800 a tashar man Dangote ba bisa ka’ida ba, lamarin da ta kira karya doka ta kasa da kuma dokokin Kungiyar Kwadago ta Duniya (ILO). Ta kuma zargi kamfanin da sauya ’yan Najeriya da ’yan kasashen waje. Saboda haka ta umarci dukkan mambobinta su dakatar da duk wani samar da gas da man zuwa Tashar Man Dangote daga ranar Lahadi, tare da gudanar da addu’o’i da zaman makoki a wuraren aiki.

Wannan yajin aikin na PENGASSAN ya tayar da tsoron karancin mai da tsadar farashi a kasuwanni, kasancewar NNPC shi ne kadai ke shigo da fetur, yayin da NMDPRA ke tsara yadda za a rarraba shi. Haka kuma NUPRC ke sa ido kan samar da danyen mai da gas ga matatun mai da kuma wutar lantarki a Najeriya. Kungiyar dillalan mai ta ce wannan mataki zai iya kawo tangarda mai tsanani ga rarraba mai a duk fadin kasar nan.

Yanzu idon jama’a da na masana ya karkata ne ga taron gaggawa da Ministan Kwadago zai gudanar a yau Litinin domin tattaunawa da bangarorin biyu. Ana sa ran wannan ganawa ce za ta kasance makomar shawo kan rikicin ko kara jefa kasa cikin tabarbarewar man fetur da wutar lantarki.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet