Featured
Gwamnan Bauchi Ya Kori Kwamishiniyar Mata Ta Jihar

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya tsige Hajiya Zainab Baban-Takko daga mukaminta na Kwamishinar Harkokin Mata da Ci gaban Yara. Mai ba Gwamna shawara kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar Litinin 29 ga Satumba, 2025.
A cewar sanarwar, tsige kwamishinar wani bangare ne na sauye-sauyen da Gwamnan ya yi a cikin Majalisar Zartarwa ta Jihar Bauchi. Gwamnan ya gode wa Hajiya Zainab bisa gudummawar da ta bayar tare da yi mata fatan alheri a ayyukanta na gaba.
Wannan na zuwa ne kasa da mako guda bayan Hukumar Kula da Ma’aikatan Jihar Bauchi ta sallami wasu manyan jami’an gwamnati biyu bisa zargin yin jabun takardu. Sanarwar ta ce laifin ya saba wa dokar Ma’aikatan Jihar Bauchi Sashe na 0327 (ii, iii da vi) wanda ya shafi yin jabun takardu da karkatar da bayanan hukuma.
Haka zalika, hukumar ta kori wani jami’in ilimi a ranar 11 ga Satumba bisa tuhumar aikata babban laifi na cin zarafin mata (sexual harassment). Wannan mataki ya nuna yadda gwamnatin jihar ke ci gaba da tsaurara doka a kan jami’an gwamnati domin tabbatar da adalci da gaskiya a ma’aikatun gwamnati.