Featured
Gwamnatin Najeriya Ta Gargaɗi Matasa Masu Hijira Daga Ƙasar Zuwa Ƙetare

Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga matasa da su guji yin hijira ta barauniyar hanya, tana jaddada cewa irin wannan tafiya na tattare da mummunan haɗari ga rayuka da ci gaban ƙasa. Ministan Ci gaban Matasa, Ayodele Olawande, ya bayyana haka a lokacin wani taron wayar da kai da aka gudanar a Abeokuta don fadakar da matasa kan illolin yin hijira ba bisa ka’ida ba. Ya ce yawancin matasa na yin irin wannan tafiya ne saboda matsalolin tattalin arziki, rashin aikin yi, rikice-rikice, da kuma burin samun damarmaki a ƙasashen waje.
Ministan, ta bakin wakiliyarsa Grace Lelea, ya bayyana cewa yawancin waɗanda ke tsallaka hamada da teku suna fuskantar mummunan ƙalubale — da dama na rasa rayukansu a Tekun Bahar Rum, yayin da wasu kuma ke fadawa tarkon masu safarar mutane, cinikin gabobi da bautar zamani. Ya ce gwamnati ta ƙaddamar da shirye-shirye da dama tare da haɗin gwiwar ma’aikatun gwamnati da ƙungiyoyin ci gaba domin bai wa matasa ƙwarewa, albarkatu da tallafin da zai sa su gina rayuwa mai inganci a gida Najeriya.
Kwamishinan Wasanni da Ci gaban Matasa na Jihar Ogun, Wasiu Isiaka, ya yaba wa gwamnatin tarayya bisa wannan shiri, inda ya ce jihar ma tana aiwatar da shirye-shiryen ƙarfafa matasa don rage sha’awar barin ƙasa ta barauniyar hanya. Haka kuma, hukumar NAPTIP ta jaddada cewa matasa ne suka fi fuskantar illolin safarar mutane da hijirar ba bisa ka’ida ba, tana kuma shawartar su su bi sahihan hanyoyi idan za su yi tafiya zuwa ƙasashen waje.
Gwamnatin Tarayya ta nanata cewa ci gaban matasa ba zai yiwu ba idan gwamnati ce kaɗai za ta ɗauki nauyi. Saboda haka ta kira iyaye, al’umma da sauran bangarori da su haɗa kai wajen gina yanayi mai inganci da zai ba matasa damar cika burinsu a cikin ƙasar.