Connect with us

Featured

Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tinubu da Naɗa Mutane Masu Takardun Bogi a Kan Muƙami

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da naɗa mutane masu takardun karatu na bogi a muƙamai. A wata wallafa da ya yi a shafinsa na X, Atiku ya nemi gudanar da bincike mai zaman kansa kan takardun karatun duka mambobin majalisar zartarwa, daga cikin su har da Shugaba Tinubu.

Atiku ya danganta murabus ɗin da Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya yi a ranar Talata da gazawar gwamnati wajen tantance ƙwararrun mutane. Ya ce kamata ya yi gwamnati ta kore shi tare da hukunta shi kan yaudara maimakon bari ya yi murabus da kansa.

Ya kuma soki Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) kan yadda ta amince da nadin Nnaji duk da cewa ita ce ta hana tabbatar da Mallam Nasir El-Rufai saboda dalilan tsaro. Atiku ya bayyana wannan a matsayin babban abin kunya ga ƙasa.

Haka kuma, Atiku ya tabo batun takardun karatun Shugaba Tinubu, yana tambaya kan yadda za a samu gaskiya idan shugabanci ya ginu kan rashin gaskiya. Ya ce lokaci ya yi da za a fitar da ƙasar daga dagwalon yaudara da mayar da martabar shugabanci. Sai dai binciken BBC ya nuna babu hujjoji masu ƙarfi da ke tabbatar da cewa takardun Tinubu na jami’ar Chicago na bogi ne.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet