Connect with us

Featured

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙudiri Aniyar Farfaɗo Da Masana’antu a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na ƙoƙarin ƙera kaya a cikin gida ” Made-in-Nigeria ” ƙarƙashin tsarin “Nigeria First”, domin farfaɗo da masana’antu da rage dogaro da kayayyakin waje. Shugaba Bola Tinubu ya bayyana haka a Lagos yayin taron Adeola Odutola na biyar da Ƙungiyar Masana’antun Najeriya (MAN) ta shirya, inda ya ce kamfen ɗin zai karkata hankalin jama’a zuwa amfani da kayayyakin da aka sarrafa a Najeriya cikin inganci, tare da samar da dubban ayyukan yi a cikin shekaru uku masu zuwa.

Tinubu ya ce gwamnati za ta ba da muhimmanci wajen sauƙaƙa harkokin masana’antu da rage kuɗaɗen tsari, domin tabbatar da cewa masana’antun Najeriya suna iya yin gasa a gida da ƙasashen waje. Ya bayyana muhimman ginshiƙai guda shida na wannan tsari: gyaran tsarin saye na gwamnati, tabbatar da inganci, faɗaɗa fitar da kaya, sauƙaƙa samun kuɗi, wutar lantarki da sufuri, horar da ma’aikata, da kuma kare kayan masarufi.

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote (ta bakin Mansur Ahmed), ya jaddada bukatar mayar da wannan tsari doka mai ɗorewa wacce ba za ta rushe da sauyin siyasa ko yanayin kasuwa ba. Ya bukaci kafa tsarin rajistar masu kaya na ƙasa, inganta tallata kayayyakin gida ga jama’a, da kuma samar da sauƙin samun kuɗi ga masana’antun cikin gida domin su iya yin gasa a kasuwannin Afirka da duniya baki ɗaya.

Shugaban MAN, Otunba Francis Meshioye, ya yaba da ƙoƙarin gwamnati wajen sauya tattalin arziki ta hanyar “Nigeria First”, yana mai cewa wannan tsari ba kawai manufar masana’antu ba ce, illa kuwa dabarar ceto tattalin arzikin ƙasa ne. Ya ce idan ba a tallafa wa masana’antun cikin gida ba, Najeriya ba za ta iya yin gasa a matakin duniya ba, saboda haka akwai buƙatar aiwatar da wannan tsari cikin doka da tsantseni.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet