Featured
Kyakkyawan Shugabancin Tinubu Ne Ya Sa Gwamnonin PDP Su Ke Tururuwar Komawa APC – Uzodimma

Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya bayyana cewa yawaitar sauya sheƙar da gwamnoni da ‘yan majalisar jam’iyyun adawa ke yi zuwa jam’iyyar APC na nuna amincewa da irin yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke gudanar da mulki. Uzodimma, wanda shi ne shugaban taron gwamnonin jam’iyyar APC, ya bayyana haka ne yayin taron shugabannin jam’iyyar a jihar Kebbi, inda ya ce wannan lamari ba bazata ba ne, illa sakamakon ayyukan da gwamnatin Tinubu ke yi.
Uzodimma ya jaddada cewa sauya sheƙar ba ta tsaya a majalisar dokoki ba kawai, har da gwamnoni daga jihohi daban-daban suna komawa APC saboda sun yarda da tafiyar gwamnatin Tinubu. Ya bayyana wannan sauyi a matsayin “wani muhimmin tarihi” da ke faruwa a kasar, inda ya yabawa Tinubu da irin rawar da yake takawa wajen farfaɗo, gyara da gina Najeriya. Ya ce shugaban zai kasance cikin tarihi a matsayin wanda ya zo, ya gani, ya kuma yi nasara.
Sauya shekar gwamnoni daga jam’iyyun adawa zuwa APC ya sauya yanayin siyasar Najeriya a ‘yan makonnin baya. A makon da ya gabata ne Gwamnan Enugu, Peter Mbah, ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC don tallafa wa shirin “Renewed Hope” na Tinubu. Hakan na zuwa ne watanni biyar bayan Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, ya sauya sheka, haka ma Gwamnan Bayelsa, Douye Diri. Haka nan ‘yan majalisa da dama daga PDP, LP da NNPP sun biyo sahu suna komawa jam’iyyar mai mulki.
Sai dai wannan gagarumin sauyi ya jawo suka daga ‘yan adawa da masu sharhi. Wasu sun bayyana shi a matsayin barazana ga tsarin jam’iyyu masu yawa, inda jam’iyyar ADC ta zargi APC da kulla dabarar “shayar da jam’iyyun adawa ruwa” don raunana su. PDP ta kuma yi zargin cewa akwai amfani da kuɗi da barazana wajen jawo mutane. Duk da haka, shugabannin APC na ci gaba da murna, inda Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya ce wannan gagarumin sauyi alamar amincewar al’umma ne da jagorancin Tinubu.