Featured
Ya Kamata Gwamnati Ta Yi Wa Ƴan Najeriya Cikakken Bayani Game Da Yunƙurin Juyin Mulki – ADC

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta bayyana gaskiyar batun zargin shirin juyin mulki da ake yadawa a ƙasar, tana mai gargadin cewa kada gwamnati ta yi amfani da lamarin a matsayin hujja don tsoratar da ’yan adawa. Kakakin jam’iyyar na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce jam’iyyar tana ɗaukar duk wata barazana ga tsarin dimokuraɗiyya da muhimmanci matuƙa.
ADC ta ce tana bin diddigin rahotannin da ke alakanta wasu jami’an soji da ake zargi da shirin juyin mulki, tare da jita-jitar cewa tsohon gwamna daga kudu yana cikin bincike bisa zargin tallafa wa waɗanda ake tuhuma. Jam’iyyar ta bayyana damuwa cewa irin wannan zargi na iya zama makarkashiya da za a yi amfani da shi wajen farautar ’yan adawa da kuma karkatar da hankalin jama’a daga matsalolin mulki.
Haka kuma jam’iyyar ta nuna rashin jin daɗi da “saƙonni masu karo da juna” daga hukumomin gwamnati, inda ta ce hedkwatar tsaro ta ƙaryata labarin juyin mulki duk da cewa kafafen yada labarai sun ruwaito akasin haka. Wannan, a cewar ADC, na iya nuni da cewa akwai siyasa a batun. Jam’iyyar ta kuma soki shiru da gwamnati ke yi game da lamarin, tana ganin hakan na iya zama dabara don karkatar da hankalin jama’a daga matsalolin tattalin arziki da rashin ingantaccen shugabanci.
ADC ta bukaci gwamnatin tarayya da ta fito fili ta bayyana gaskiyar lamarin, tana mai cewa idan akwai gaskiya a zargin barazanar tsaro, ya kamata gwamnati ta sanar da ’yan ƙasa gaskiya ta kuma yi cikakken bayani. Jam’iyyar ta jaddada cewa ba za ta taɓa goyon bayan kowace irin mulkin kama-karya ba, ko ta sojoji ko ta farar hula, amma tana adawa da amfani da batun tsaro wajen murƙushe ’yancin faɗin albarkacin baki ko ra’ayin siyasa.