Featured
Sauya Sheƙa Ba Shi Ke Nuna Jam’iyyar Da Za Ta Lashe Zaɓe Ba — Ibrahim Mani

Jigon jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Dr. Ibrahim Mani, ya bayyana cewa jam’iyyarsu ba ta damu da yawaitar sauya shekar ‘yan siyasa zuwa jam’iyyar APC ba, domin, a cewarsa, “yawan jam’iyya ba shi ne ke yanke hukuncin zaɓe ba, sai dai ra’ayin al’umma.” Mani ya ce ‘yan Najeriya sun gaji da halin tattalin arzikin ƙasar, kuma za su nuna damuwarsu a zaɓen 2027 ta hanyar kuri’a, ba ta hanyar bin masu sauya sheka ba.
Ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Trust TV, inda ya ce duk da cewa wasu gwamnoni da manyan ‘yan siyasa suna sauya sheka, hakan ba yana nufin jama’ar jiharsu za su bi sahunsu. “Mutane sun san abin da suke so, kuma sun san yadda gwamnati ta gaza. Saboda haka, ba sauya sheka ba ne zai yanke hukuncin wanda zai yi nasara, amma jama’a ne,” in ji shi.
Dr. Mani ya kuma jaddada cewa jam’iyyar ADC ba ta goyon bayan duk wani yunkurin kifar da gwamnati ta hanyar karfi ko juyin mulki, yana mai cewa jam’iyyar na da yakinin cewa tsarin demokuradiyya a Najeriya yana ƙara ƙarfi da kwarewa. Ya ce, “hanya ɗaya tilo da za a iya canja gwamnati ita ce ta akwatin zaɓe, ba ta bindiga ba.” Ya gargadi ‘yan siyasa da ke yayata jita-jitar juyin mulki da su guji tada hankalin jama’a, domin hakan na iya jefa ƙasar cikin rudani.
A ƙarshe, Mani ya ce ADC na aiki don gina jama’a da zai ba ‘yan Najeriya damar su karɓi ikon ƙasarsu ta hanyar kuri’a, ba ta hanyar sauya jam’iyya ba. Ya ce sauya sheka ba ya magance matsalolin ƙasa kamar tsadar rayuwa, rashin tsaro da talauci, waɗanda ke ci gaba da addabar al’umma. “Abin da muke so shi ne sauyi ta hanyar zaɓe na gaskiya da adalci, wanda zai inganta rayuwar ‘yan ƙasa,” in ji shi.