Connect with us

Featured

Da Ɗumi-ɗumi : Tinubu Ya Kori Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi sauye-sauye a manyan mukaman tsaro na ƙasar, inda ya sauke Janar Christopher Musa daga matsayin Babban Hafsan Tsaro na Ƙasa tare da wasu shugabannin rundunonin soja. Wannan mataki ya biyo bayan wani umarni da fadar shugaban ƙasa ta fitar a ranar Juma’a, wanda mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai, Sunday Dare, ya sanya hannu.

A cikin sanarwar, an bayyana cewa Janar Olufemi Oluyede, wanda kafin haka shi ne Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, yanzu shi ne sabon Babban Hafsan Tsaro na Ƙasa. Haka kuma, an naɗa Major-General W. Shaibu a matsayin sabon Babban Hafsan Soja, yayin da Air Vice Marshall S.K. Aneke ya zama sabon Babban Hafsan Sojin Sama, sai Rear Admiral I. Abbas da aka naɗa Babban Hafsan Rundunar Ruwa.

Sai dai Babban Daraktan Leken Asirin Tsaro (Chief of Defence Intelligence), Major-General E.A.P. Undiendeye, ya ci gaba da rike matsayinsa kamar yadda yake a baya. Shugaba Tinubu ya bayyana godiyarsa ga tsoffin hafsoshin bisa rawar da suka taka wajen kare tsaron ƙasar da jajircewar da suka nuna a lokacin aikinsu.

Shugaban ƙasar ya kuma umarci sabbin hafsoshin da su tabbatar sun nuna ƙwarewa, tsantseni, da haɗin kai a tsakanin rundunonin tsaro, domin ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa da tabbatar da zaman lafiya a fadin Najeriya.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet