Connect with us

Featured

Sauya Hafsoshin Tsaro Bashida Alaƙa Da Zargin Yunƙurin Juyin Mulki – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa cire hafsoshin tsaro da shugaba Bola Tinubu ya yi ba shi da alaƙa da jita-jitar yunkurin juyin mulki, sai dai wani mataki ne kawai na inganta rundunonin soji. Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin labarai, Bayo Onanuga, ya ce Tinubu yana da cikakken ikon sauya hafsoshin tsaro duk lokacin da ya ga dama domin inganta aiki a rundunar.

A cikin sanarwar da mai ba da shawara na musamman kan yada labarai, Sunday Dare, ya fitar, an bayyana janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon shugaban rundunar tsaro na ƙasa, wanda ya maye gurbin Janar Christopher Musa. Dare ya ce sauran sabbin shugabannin sun haɗa da Manjo Janar W. Shaibu (Sojojin Ƙasa), Air Vice Marshal S.K. Aneke (Sojojin Sama), da Rear Admiral I. Abbas (Sojojin Ruwa). Shugaban leken asiri na tsaro, Manjo Janar E.A.P. Undiendeye, ya ci gaba da rike mukaminsa.

Sai dai cire hafsoshin ya jawo cece-kuce, musamman ganin cewa an yi shi ne mako guda bayan wata jarida ta wallafa labarin cewa wasu jami’an soja suna shirya juyin mulki. Duk da rundunar soji ta musanta labarin, jama’a da ‘yan adawa sun ci gaba da ganin akwai alaƙa. Jam’iyyar ADC ta nemi fadar shugaban ƙasa ta fayyace hakikanin dalili, tana mai cewa irin wannan sauyi yana da tasiri ga kwanciyar hankali a cikin rundunonin tsaro.

Masana harkokin tsaro kuwa sun bayyana ra’ayoyi mabambanta. Wasu sun ce wannan sauyi zai ƙarfafa gwiwar sabbin hafsoshi wajen gudanar da aiki, yayin da wasu suka yi gargadin cewa sauya shugabanci ba zai magance matsalar tsaro ba idan ba a inganta yanayin aiki da walwalar sojoji ba. Sun bukaci sabbin hafsoshin su mayar da hankali wajen tabbatar da jin daɗin ma’aikata da kuma kyautata tsarin aiki domin samun nasara.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet