Featured
Ana Zargin Tsohon Gwamnan Bayelsa Da Hannu a Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaron soji sun kama wani Manajan Darakta na wata hukumar gwamnatin tarayya a yankin Kudu maso Kudu bisa zargin sa da tura makudan kuɗaɗe zuwa hannun tsohon Ministan Albarkatun Mai, Timipre Sylva, domin tallafa wa shirin juyin mulki a ƙasar. Majiyoyi sun ce ana tuhumar daraktan ne da aikata wannan ɗanyen aiki, inda ake zargin an tura kuɗaɗen ne don taimaka wa waɗanda ke shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
A cewar bayanai daga hukumomin leƙen asiri, an kai samame gidan Sylva da ke Abuja a ranar Asabar, inda aka kama ƙaninsa Paga Sylva wanda shi ne mataimakinsa na harkokin cikin gida, tare da direbansa. Rahotanni sun ce Sylva ba ya ƙasar lokacin da aka kai samamen, kuma ya janye shirin dawowarsa bayan ya samu labarin cewa an kama wasu sojojin da ake zargi da hannu a shirin juyin mulkin.
Hukumar tsaron soja ba ta bayar da wata sanarwa kai tsaye ba kan lamarin, sai dai a baya Kakakin sojoji, Brig-Gen Tukur Gusau, ya bayyana cewa an kama jami’ai 16 bisa laifin karya dokokin aiki da rashin ladabi, ba wai juyin mulki ba. Duk da haka, rahotannin wasu kafafen labarai irin su SaharaReporters sun ce jami’an da aka kama – daga mukamin Kyaftin zuwa Janar – na cikin waɗanda ke shirin kifar da gwamnati.
Lamarin ya tayar da hankula a fagen siyasa da tsaro, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan ko akwai manyan jami’an gwamnati ko masu hannu da shuni da suka taka rawa wajen ɗora wannan zargi mai nauyi da ka iya girgiza gwamnati mai ci.
Tushen Labari : The Punch.