Connect with us

Featured

Majalisar Wakilai Ta Amince Tinubu Ya Ciyo Bashin Dala Biliyan $2.34

Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da bukatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na neman rance dala biliyan $2.34 daga kasuwannin kudi na duniya domin cike gibi a kasafin kudin shekarar 2025 da kuma biyan bashin Eurobond da zai kare nan gaba. Wannan kuduri ya samu sahalewar majalisar ne bayan karanta rahoton kwamitin tallafi, lamuni da kula da bashi na kasa, karkashin jagorancin Hon. Abubakar Hassan Nalaraba, a zaman majalisar da Kakakin Majalisa Tajudeen Abbas ya jagoranta.

Rahoton kwamitin ya bayyana cewa daga cikin kudaden da za a ranto, dala biliyan $1.23 za a yi amfani da su wajen cike gibin kasafin kudin bana, yayin da saura dala biliyan $1.12 za su tafi wajen biya da sabunta Eurobond da zai kai lokacin biyan sa a watan Nuwamba 2025. An bayyana cewa kudaden za a iya samu ta hanyar fitar da Eurobond, hadin gwiwar lamuni, ko kuma ta hanyar cibiyoyin kudi na duniya kai tsaye.

Haka kuma, majalisar ta amince da shirin gwamnatin tarayya na fitar da Sovereign Sukuk na farko da Najeriya za ta taba fitarwa a kasuwannin duniya, wanda zai kai kimanin dala miliyan $500, tare da yiwuwar samun tabbacin lamuni daga wasu cibiyoyin kudi.

Shugaba Tinubu ya bayyana a wasikar da ya aikawa majalisar cewa wannan mataki na neman rance ya zama dole ne domin gwamnati ta iya aiwatar da shirinta na 2025 yadda ya kamata, da kuma tabbatar da cewa Najeriya ta biya basussukan da suka kai lokacin biyan su ba tare da tangarda ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet