Featured
Sama Da Mutane 170 Daga Kasashen Ƙetare Ne Ke Son Zama Ƴan Najeriya – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta ce tana tantance ’yan ƙasashen waje 170 da ke neman zama ’yan Najeriya, inda ta jaddada cewa sai wanda ke da kyakkyawan hali da nagartaccen suna ne za a amince da shi. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana haka a Abuja bayan taron Kwamitin Shawarwari kan Batun Ƙasa (Citizenship Advisory Committee) wanda ke tantance irin waɗannan buƙatu kafin a tura su ga Shugaba Bola Tinubu domin amincewa.
Tunji-Ojo ya ce Najeriya ba ƙasa bace da kowa zai samu takardar zama ɗan ƙasa kawai saboda ya nema, yana mai cewa wanda zai rike takardar zama ɗan Najeriya dole ne mutum ne mai ƙima, ɗabi’a, da gaskiya. Ya kara da cewa akwai kwamitin da ke kunshe da jami’an DSS, Hukumar Shige da Fice (NIS), Ma’aikatar Shari’a, da Ma’aikatar Harkokin Waje da ke gudanar da cikakken bincike kafin amincewa da kowanne mai nema.
Ministan ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu tana ƙoƙarin gina ƙasa da za ta zama abin alfahari ga ’yan ƙasa da kuma abin koyi a idon duniya. A cewarsa, manufar gwamnati ita ce ta gina Najeriya mai nagarta, tsari, da ci gaba wadda za ta jawo hankalin kowa, amma ba ta hanyar buɗe ƙofa ga duk mai son zama ɗan ƙasa ba.