Featured
UBA Ya Samu Ribar Naira Tiriliyan 2.47 a Cikin Watanni Tara

Babban bankin United Bank for Africa (UBA) ya bayyana cewa ya samu jimillar kuɗaɗen shiga na Naira tiriliyan 2.47 a cikin watanni tara na farko na shekarar 2025, wanda ke nuna cewa an samu ƙari idan aka kwatanta da N2.40 tiriliyan da aka samu a daidai wannan lokaci na 2024. A cewar rahoton kuɗin bankin da aka gabatar ga Nigerian Exchange Limited, ribar bayan haraji ta tashi zuwa N537.5 biliyan daga N525.3 biliyan a bara — ƙaruwa da kaso 2.3 cikin ɗari.
Bankin ya bayyana cewa samun kuɗaɗen shiga daga riba (interest income) ya karu zuwa N1.98 tiriliyan saboda hauhawar kudaden da aka samu daga lamuni da saka hannun jari, duk da cewa kudin da ake biya a matsayin riba (interest expenses) ya karu zuwa N808.7 biliyan saboda tsadar hanyoyin samun kuɗi. Haka kuma, jimillar kadarorin bankin ta tashi zuwa N32.49 tiriliyan daga N30.32 tiriliyan a ƙarshen 2024, yayin da hannun jarin masu zuba jari (shareholders’ funds) ya kai N4.3 tiriliyan.
Duk da ƙaruwa a ribar, kudaden gudanarwa (operating expenses) sun tashi zuwa N846.1 biliyan daga N812.2 biliyan. Rahoton ya kuma nuna cewa bankin ya samu ci gaba a ajiyar riba (retained earnings), wanda ya kai N1.77 tiriliyan — alamar dorewar habakar kasuwanci a sassa daban-daban na Afirka da kasashen ketare.
UBA ta kuma tabbatar da cewa tana da cikakken bin ƙa’idar kasuwar hannayen jari ta Najeriya (NGX), inda ta sanar da kashi 84.36 cikin ɗari na hannayenta suna cikin kasuwar buda kai (free float). Duk da kasancewar tana cikin ƙarar shari’a sama da 1,700, bankin ya ce babu hatsarin da zai kawo babban asara bayan shawarwarin lauyoyi.