Connect with us

Featured

Gwamnatin Kano Ta Amince Da Kashe Naira Biliyan 8.2 Don Inganta Ilimi, Ruwa da Makamashi

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe sama da Naira biliyan 8.2 domin aiwatar da muhimman ayyuka a fannonin ilimi, samar da ruwan sha da kuma makamashi a faɗin jihar. Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature, ya bayyana cewa an cimma wannan matsaya ne yayin zaman majalisar zartarwa ta jihar karo na 33 ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

A cewar Bature, sama da Naira biliyan 4.9 za a kashe su wajen farfaɗo da harkar ilimi, da suka haɗa da gyaran Makarantar Kere-Kere ta Ungogo (Phase II), samar da kayan koyarwa ta hanyar gidan buga littattafai na jihar, da kuma kammala da ɗora kayan aiki a e-library na Kwalejin Ilimi da Nazarin Farko. Haka kuma za a sayi kayan ofis ga Jami’ar Arewa maso Yamma (Northwest University) domin inganta aiki.

Haka nan majalisar ta amince da kashe Naira biliyan 3.3 don ayyukan samar da ruwa da makamashi, ciki har da gina sabuwar cibiyar tace ruwa a Taliwaiwai, ƙaramar hukumar Rano. Za a kuma biya bashin lantarki da mai na hukumar ruwa, da kuma kula da injinan tace ruwa domin tabbatar da ci gaba da samun ruwan sha mai tsafta.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa ayyukan da ke tasiri ga rayuwar al’umma muhimmanci, musamman waɗanda ke inganta ilimi, kiwon lafiya da walwalar jama’a a faɗin Kano.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet