Connect with us

Featured

Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Wani Mutum a Gombe

Hatsari ya auku a kan hanyar Cham–Numan da ke cikin karamar hukumar Balanga a jihar Gombe, inda mutum ɗaya ya rasa ransa, ɗaya kuma ya ji rauni, yayin da wasu huɗu suka tsira ba tare da wani rauni ba. Hukumar FRSC ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin 03 ga Nuwamba, tana mai cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudu fiye da ƙima da kuma kasa sarrafa mota.

Kwamandan hukumar a jihar, Samson Kubara, ya bayyana cewa motar da ta yi hatsarin ita ce Toyota Camry, kuma an garzaya da gawar wanda ya mutu zuwa cibiyar lafiya ta Primary Health Care, Cham, domin ajiya. Ya kuma yi kira ga direbobi su guji yin gudu saboda neman ƙarin kuɗi da wuri, yana mai cewa “duk wanda ya mutu ba zai ci kuɗi ba.”

Kubara ya jaddada muhimmancin bin ƙa’idojin hanya, yana shawartar direbobi su sanya na’urar iyaka gudu (speed limiter) a motocinsu, tare da tabbatar da cewa sun duba lafiyar motarsu kafin tafiya. Ya ce hanyar Cham–Numan tana da duwatsu da gangare, don haka akwai buƙatar direbobi su yi taka-tsantsan yayin tuƙi.

Hukumar FRSC ta kuma sake jan kunne ga direbobi da su guji dibar kaya da fasinja fiye da kima, tare da bin ƙa’idar tuki domin kare rayukansu da na sauran masu amfani da hanya. An ce tuki cikin kulawa da bin doka ita ce hanya guda tilo ta guje wa irin waɗannan haɗurra da ke janyo asarar rayuka da dukiya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet