Connect with us

Featured

Ban Taɓa Zargin Shettima Da Ƙirƙiro Boko Haram Ba – Ali Modu Sheriff

Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya musanta rahotannin da ke cewa ya taɓa zargin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da ƙirƙiro kungiyar Boko Haram. A wata sanarwa da ya fitar, Sheriff ya bayyana labarin a matsayin ƙarya marar tushe da wasu ke ƙoƙarin yaɗawa don tada fitina da kawo rabuwar kai a tsakanin al’umma.

Ya ce bai taɓa yin wata hira ko yin bayani da ya shafi danganta Shettima da kafa Boko Haram ba. Sheriff ya ce waɗanda suka yaɗa wannan labari na ƙoƙarin rage masa ƙima da kuma ɓata gudunmawar da yake bayarwa wajen samar da zaman lafiya da haɗin kai a Jihar Borno da ma Najeriya baki ɗaya.

Sheriff ya bayyana cewa tuni ya umarci lauyoyinsa su gano waɗanda suka yaɗa labarin domin ɗaukar matakin shari’a a kansu. Ya kuma yi gargadin cewa idan ba a gaggauta cire labarin daga kafafen da suka wallafa ba, zai ɗauki mataki kai tsaye ta hanyar kotu.

A ƙarshe, ya roƙi ’yan Najeriya da kafafen watsa labarai da su yi taka-tsantsan wajen yaɗa bayanai, inda ya bukaci su rika bin gaskiya da adalci domin kaucewa yaɗa abubuwan da za su iya jawo rikici ko rashin jituwa tsakanin jama’a.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet