Featured
Ƴan Bindiga Sun Sako Mataimakin Kakakin Majalisar Kebbi

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Muhammad Sama’ila Bagudo, ya koma cikin iyalansa bayan shafe kwanaki a hannun masu garkuwa. Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ta tabbatar da sakin nasa a jiya Lahadi, inda ta ce an mika shi ga likitoci don duba lafiyarsa kafin ya koma gida.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ya bayyana cewa hadin gwiwar jami’an tsaro daban-daban da kuma bayanan sirri daga al’umma ne suka taimaka wajen ceto Bagudo lafiya. Ya yaba wa mutanen jihar bisa goyon bayan da suka bayar, tare da jinjinawa jaruntakar jami’an tsaron da suka shiga aikin.
Rundunar ta ce za ta ci gaba da kai dauki kan ayyukan ‘yan bindiga a sassan jihar, kana ta bukaci jama’a su ci gaba da sanya ido da bayar da rahoton duk wani abin da ake zargi domin dakile barazana kafin ta girma.
An sace Bagudo ne a ranar 31 ga Oktoba 2025, bayan ya kammala sallar Isha’i a garinsu Bagudo, hedikwatar Karamar Hukumar Bagudo. Sakin nasa ya zo daidai da lokacin da aka gudanar da addu’o’in hadin kai tsakanin Musulmai da Kiristoci a Birnin Kebbi, domin neman zaman lafiya a jihar.