Featured
Soludo Ya Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra a Karo Na Biyu

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Charles Soludo na jam’iyyar APGA, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar 8 ga Nuwamba 2025. Sakamakon da aka tattara a cibiyar ƙididdigar sakamako da ke Awka, babban birnin jihar, ya nuna cewa Soludo ya samu kuri’u 422,664, inda ya sha gaban sauran ‘yan takarar da tazara mai nisa.
Dan takarar jam’iyyar APC, Nicholas Ukachukwu, ya zo na biyu da kuri’u 99,445, yayin da George Moghalu na jam’iyyar Labour Party (LP) ya samu kuri’u 10,576. Dan takarar PDP, Jude Ezenwafor, ya zo a matsayi na huɗu da kuri’u 1,401 kacal.
Returning Officer na zaben, Farfesa Edoba Omoregie, ya bayyana cewa zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali, tare da cika dukkan sharuddan doka. Ya ce Soludo ne ya fi kowanne yawan kuri’un da suka halatta, saboda haka ya cancanci a dawo da shi gwamna bisa ƙa’ida.
Jam’iyyar APGA da magoya bayanta sun bayyana farin ciki kan nasarar, inda suka ce wannan alama ce ta ci gaba da goyon bayan jama’a ga gwamnatinsu.