Addini
NAHCON Ta Rage Kuɗin Kujerar Aikin Hajjin 2026

Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta sanar da cewa an rage kudin aikin Hajji na shekarar 2026, bayan shawarar da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayar domin saukake wa alhazai. Kafin saukin, masu tafiya daga kudu na biyan sama da N8.7m, yayin da na Arewa ke biyan kusan N8m.
Sabon tsarin ya nuna cewa alhazai daga kudu za su samu mafi girman ragi har N792,943, inda yanzu za su biya N7,991,141.76 maimakon N8,784,085.59 da ake biya a baya. Haka nan na yankin Arewa za su ga ragin N760,915.83, wanda zai saukar da kudin su zuwa N7,696,769.76.
Bugu da kari, yankin Borno da Adamawa sun samu mafi karancin farashi kasa da kowa, inda yanzu kudin ya tsaya kan N7,579,020.96 bayan an rage N748,104.63. Wannan sabon farashi, a cewar hukumar, zai taimaka wa dubban musulmi su kusanci samun damar zuwa aikin Hajji.
NAHCON ta kuma bayyana cewa ranar 5 ga Disamba, 2025 ita ce ranar karshe da za a karbi kudaden alhazai domin kammala shiri da tabbatar da kujeru. Hukumar na fatan wannan saukin zai karfafa gwiwar masu niyyar zuwa ibadar wannan shekara.