Featured
Zargin Yunƙurin Kashe Lt. Ahmed Yerima Ba Gaskiya Bane – Rundunar Ƴansanda

Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya ta nesanta kanta daga rahotannin da ke yawo cewa an yi yunkurin kashe wani jami’in Rundunar Ruwa, Lt. Ahmed Yerima, a Abuja. Wannan ya biyo bayan labaran da wasu kafafen yada labarai suka yada cewa an bi diddigin jami’in a cikin motocin Hilux biyu marasa lambar ƙasa daga hanyar Kubwa zuwa Gado Nasco Way. ’Yan sanda sun bayyana cewa babu wani rahoto ko bayanin faruwar haka a duk fadin FCT, kuma jama’a su guji yada labaran da ba a tabbatar ba.
Zargin yunkurin kisan ya tayar da ƙura ne bayan rikicin da ya barke tsakanin Yerima da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kan wani fili a Gaduwa District da ake zargin mallakin tsohon Hafsan Rundunar Ruwa, Vice Admiral Zubairu Gambo (rtd). A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu, an ga Yerima yana takawa tawagar ministan burki, inda Wike ya zarge shi da hana jami’an FCDA daukar matakin rushe gine-ginen da ake yi ba bisa ka’ida ba. Ministan ma ya yi zafafan maganganu, yana kira wa jami’in da “wawa”.
Lamarin ya raba jama’a gida biyu, wasu na ganin Wike ya yi aiki ne bisa doka, yayin da wasu kuma—musamman tsofaffin hafsoshin soja—ke goyon bayan Yerima, suna mai cewa bai kamata a hukunta shi ba. Wasu ma sun nemi a nemi afuwa daga ministocin gwamnati saboda cin zarafin jami’in da ya ke bakin aiki.
Ministan Tsaro, Mohammed Abubakar, ya tabbatar cewa duk jami’in soja da ke aiwatar da aikinsa bisa ka’ida ba zai fuskanci hukunci mara tushe ba. Ya ce gwamnati za ta kare mutuncin dakarun da ke gudanar da ayyukansu yadda doka ta tanada, musamman yayin shirye-shiryen bikin tunawa da sojojin Najeriya na 2026.