Featured
Ƴan Bindiga Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta Sun Yi Garkuwa Da Ɗalibai 25 a Kebbi – Rundunar Ƴansanda

’Yan sanda sun tabbatar da harin da aka kai wa Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Comprehensive da ke Maga, Jihar Kebbi, inda aka kashe Mataimakin Shugaban Makarantar sannan aka yi garkuwa da dalibai. Lamarin ya faru ne da sassafe ranar Litinin, lokacin da maharan suka tsallaka katangar makarantar dauke da manyan makamai, suka fara harbe-harbe sannan suka yi awon gaba da dalibai 25 daga dakunan kwanan su.
Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya ce an tura rundunonin ’yan sanda domin yin artabu da maharan, amma tuni suka tsere da waɗanda suka sace. Ya ƙara da cewa harin ya zo ne a lokacin da ake fama da wasu sauran hare-hare da al’ummar yankin suka shafe makonni suna fuskanta.
A cewar Gwamnatin Jihar Kebbi, Mataimakin Gwamna, Sanata Umar Tafida, ya tafi yankin don tantance halin da ake ciki domin ya wakilci Gwamna Nasir Idris wanda baya jihar a halin yanzu. Hakazalika, mazauna yankin sun bayyana takaici da alhini, inda wani mazauni, Aliyu Yakubu, ya ce harin ya faru ba tare da an sami wata ƙwakkwaran kariya ba.
Wani babban abin bakin ciki shi ne jikkatar da aka yi wa Shugaban Makarantar, Malam Makuku, wanda aka harba yayin da yake ƙoƙarin kare dalibansa. A cewar mazauna yankin, wannan abu babban rashi .