Connect with us

Featured

Ƴan Bindiga Sun Sace Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Sama’ila-Bagudo, a daren Juma’a a garin Bagudo. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:20 na dare, jim kaɗan bayan ya idar da sallar Isha’i, a yayin da yake kan hanyarsa ta komawa gida.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar, CSP Nafi’u Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi ranar Asabar 01 ga Nuwamba. Ya ce, tuni rundunar ta haɗa gwiwa da jami’an soji da masu gadin gari domin bin sawun masu garkuwar tare da tabbatar da ceto lafiyayyen dan majalisar.

Abubakar ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Bello Sani, ya tabbatar da kudirin rundunar wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Ya kuma roƙi al’umma su ci gaba da ba jami’an tsaro goyon baya da bayanai masu amfani don tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar.

A halin yanzu dai ba a bayyana bukatun masu garkuwar da kuma matakin da gwamnati ta ɗauka ba. Rahotanni sun ce jami’an tsaro suna ci gaba da sintiri da bincike a dazukan da ake zargin ‘yan bindigar suka nufa domin ceto Mataimakin Kakakin daga hannunsu cikin koshin lafiya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet