Connect with us

Addini

Gwamnatin Katsina Ta Shirya Muƙabala Tsakanin Masussuka Da Malaman Jihar

Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana shirinta na gudanar da zama na musamman tsakaninta da fitaccen malamin addini, Sheikh Yahya Masussuka, da kwamitin malaman jihar, domin jin bayani kan wasu kalaman da ake zarginsa da furtawa a karatuttukansa. Sanarwar da gwamnatin ta fitar ta nuna cewa an gayyaci malamin domin ya yi bayanin kare kansa game da waɗannan zarge-zarge.

Tun farko wasu malamai a jihar ne suka shigar da ƙorafi ga hukuma, suna zargin Sheikh Masussuka da wuce gona da iri a wasu wa’azuzzukansa. Wannan ƙorafi ya jawo martani daga wasu malamai da ke goyon bayan Sheikh ɗin, waɗanda su ma suka shigar da nata ƙorafin, suna zargin cewa ana yi wa malamin barazana tare da cin mutunci.

Gwamnatin ta ce zaman da za a gudanar zai ba kwamitin damar sauraron bangarorin biyu domin tantance gaskiyar al’amari cikin adalci da natsuwa. Haka kuma, ta bayyana cewa za a yi nazari kan tsarin wa’azi a jihar domin kauce wa rikice-rikice da sabani a nan gaba.

A cewar sanarwar, bayan kammala wannan zama, za a samar da ƙa’idojin wa’azi da za su zama doka a fadin jihar. Gwamnati ta kuma yi gargadin cewa duk wanda ya saba wa waɗannan ƙa’idoji zai fuskanci hukunci domin tabbatar da zaman lafiya da daidaito a harkokin wa’azi.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet